- introduction
- picture
- Boutique
- Related
Developer's DescriptionBy VOA (Voice of America)An kafa sashen Hausa na Muryar Amurka ran 21 ga watan Junairu, shekara ta 1979, domin watsa labaran duniya da shirye-shirye zuwa ga Hausawa da...An kafa sashen Hausa na Muryar Amurka ran 21 ga watan Junairu, shekara ta 1979, domin watsa labaran duniya da shirye-shirye zuwa ga Hausawa da masu jin harshen Hausa a duk fadin duniya, musamman ma yammacin Afirka kamar kasashen Nigeria, Ghana, Nijar, Chadi, Libya, Cote dIvoire da wasu sassan janhuriyar Benin. Sashen Hausa na watsa saoi 13.5 na shirye-shirye a kowace mako, ta radiyo da yanar intanet. Sashen kuma na buga labaran gida Najeria, da sauran duniya, da bidiyon manyan labaran Afirka daga ran Litinin zuwa Jumaa akan shafinsa na intanet. Shirye-shiryen sashen sun hada da labarai masu zafi , da rahotannin wakilai daga duk fadin duniya, tattaunawa da manyan jamian gwamnatoci, ganawa da masu fashin baki, fadakarwa daga malamai da manazarta, dauka da watsa raayoyin masu sauraro da suke bayarwa a rubuce, ta waya kai tsaye da kuma ta email.